Iraqi ta ce ta gayyaci shugaban sufetoci masu duba makamai na Majalissar dinkin duniya, Hans Blix, ya je Baghdaza domin shawarwari a cikin watan Janairu. Kotun soji a Russia ta yanke hukuncin cewa, babban jami'in sojin da ake zargi da aikata laifuka kan farar hulla a Chechnya bashi da laifi. A Najeriya Jam'iyar PDP mai mulkin kasar ta bayyana shirye-shiryenta na fitar da dan takarar shugaban kasa a babban taron jamiyyar da za'a fara ranar juma'a mai zuwa, a Abuja babban birnin kasar.